DAN MAJALISAR MAI WAKILTAR MAZABAR FUFORE/SONG a MAJALISAR TARAYYA YA SAKE YIN FITAN BARDEN GUZA DOMIN CIRE AL'UMMAR HIRNANGE CIKIN DUHU FA SUKE CIKI NA TSAWON LOKACIN INDA DAN MAJALISAR YA KAWO MUSU SABUWAR TIRANSiFOMA MAI KARFI 500KVA.
Cikin Ikon Allah da Amincewar Shi Barista Aliyu Wakili boya ya sake Bawa Yan Siyasa Mamaki Bayan Abubuwa Da yayi Abaya Na Sanya al'ummar da yake wakilta farin ciki da Jin dadi. Akwai wasu rahotanni dake cewa yanzu haka mazauna Hirnange dake Gurin sun cika da farin ciki tare da mika godiya ga Hon. Aliyu Wakili Boya.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Fufore/Song a majalisar tarayya ya sake yin fitan Barden guza Domin cire al'ummar Hirnange cikin duhu fa suke ciki Na tsawon lokaci inda Dan majalisar ya kawo musu sabuwar tiransifoma mai karfin 500KVA.
Hirnange dake Gurin a karamar hukumar Fufore sun shafe sama da shekara guda a cikin duhu bayan da taranfomar tasu ta kone, yayin da aka sace mahimman na'urar cikin ta.
Wannan Batu ne dai, ya shiga kunnuwan Dan majalisar Nan take kuwa, ya sha alwashin maye musu gurbin taransfoma tasu ta Baya fa Bata wuce 300kva ba da sabuwar Na karfin 500kva, ya dai cika alkawarin ne ranar Asabar 7 ga watan Disamban wannan Shekarar.
A yanzu dai ilahirin al'ummar garin Hirnange dake Gurin na cikin farin cikin Bayan irin kokarin da Wakili boya yayi domin ganin hasken wutan lantarki.
Wanda suka Kira a matsayin gagarumin cigaba a gare su. Sun Kuma Mika godiyar su ga Hon. Aliyu Wakili Boya. Tare yiwa Barista alkawarin Goya masa Baya a dukkan mukamin da Zai nema nan gaba.
Har ilayau a cigaba da Sanya farin ciki da Barista Aliyu Wakili boya yake yiwa jama'ar Shi da yake wakilta a majalisar wakilai
A yanzu haka suma al'ummar yankin Tinde Laro Suna cikin wadanda Dan majalisar ya Sha alwashin kawo hasken wutan lantarki Bayan da Dan majalisar ya kawo musu na'urar haska wuta na ranq tare a mazabar Dirma dake Fufore.
Yunkurin na Boya, Na kawar duhu a Tinde Laro dake Yankin Yungur Dirma aikin Na gudana ne a karkashin jagorancin Hon Abaye da tawagar shi domin tabbar da an kai wutan haskaka titi Mai anfani da Rana inda ya dace.
Al'ummar Yungur Sun Nuna Jin Dadin Su bisa irin wannan gagarumin aikin day Dan majalisar Hon Aliyu Wakili boya tare da jinjina mishi Akan irin aiyukan ci gaba da yake kaiwa al'ummar Dan yake wakilta a majalisar dokokin kasar.
Wandannan cigaban Wani bagare ne Na yunkurin da Dan majalisar yake domin Ƙarfafa tsoro tare da haɓaka kasuwanci da sauran sa'o'i tare fa kare rayuwa ka da dukiyoyin al'ummar yankin Dama Adamawa baki daya.
A yanzu dai sakanin al'ummar Fufore fa Song ba Abunda ya rage Sai godiya tare da nasara GA Dan majalisar.
Babban abun jira a Gani shine yunkurin Boya Na gaba.
Wannan sanarwa ya fito ne Daga office kungiyar Boya Moving train jirgin da ya dokufa wajen Canza Rayuwar nagartattun al'ummar Fufore Da Jihar Adamawa Gaba Daya
Abubakar Sali
#boyamovingtrain
Comments
Post a Comment