SABUWAR SHEKARA (2025) DAGA HON. (BAR.) ALIYU WAKILI BOYA DAN MAJALISAR TARAYYA MAI WAKILTAR FUFORE/SONG A MAJALISAR KASA, DAKE WAKILTAR AL'UMMAR MAZABAR FUFORE/SONG

SABUWAR SHEKARA (2025) DAGA HON. (BAR.) ALIYU WAKILI BOYA DAN MAJALISAR TARAYYA MAI WAKILTAR FUFORE/SONG A MAJALISAR KASA, DAKE WAKILTAR AL'UMMAR MAZABAR FUFORE/SONG
*****

Ya ku jama'ata na Fufore da Song.

Ina mai matukar farin ciki da girmamawa da farko ina yiwa daukacin al'ummar Fufore da Song barka da shiga sabuwar shekara ta 2025, sannan barka da sabuwar shekarar ga alummar jihar Adamawa da Najeriya baki daya. Ina muku Fatan kasancewa cikin farin ciki da kuma cimma nasarori da kuma dukkan abunda kuka saka a gaba a cikin wannan shekarar ta 2025, da shekaru masu zuwa.

Barkan mu da Shiga sabuwar shekara ta 2025!!!

Ga dukkanmu ya kamata mu godewa Allah kasancewar mu cikin 2025, ya dace mu yarda da ikon Allah wanda ya kawo mu wannan Shekara cikin koshin lafiya.

Don haka, yayin da muke bankwana da shekarar 2024 zuwa 2025, ya kamata mu godewa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu ikon shiga wannan shekarar cikin koshin lafiya.

Mu tallafa wa Gwamnati mai ci a kowane mataki ko ta halin kaka. Kada a yaudare mu da tsadar rayuwa da aka fuskanta a 2024; kalubalen ba Najeriya kadai ta shiga wannan hali ba, ya nayi ne da duniya gaba daya ta shiga. Da yardar Allah tsadar rayuwa da ake ciki zai ragu a wannan shekarar ta 2025.

Ina kira ga matasan mu, kada mu ce aikin Gwamnati kadai zamu jira, zamanin da kowa yake nemawa kan shi mafita. A cikin ƙasashen da suka ci gaba, mutane kaɗan ne ke aiki a matsayin ma'aikatan gwamnati, yayin da yawancin su ke dogara da kansu har ma su zama masu ɗaukar ma'aikata.

Kyakkyawar tarihin da muke bari a 2024 a fadin mazabar mu ya wuce abunda zamu ammbata da kalma. Waɗannan su ne ƙwaƙƙwaran hujja da zamu buga misali da shi cewar muna aiki tukuru tare sadaukar da kai domin kawo sauyi a jagorancin da muke, tare nuna ingantaccen wakilci kamar yadda muka yi muku alkawari a baya.

Muradun ku da bukatunku a ko yaushe shine babban abunda ke gaban mu, kuma a wannan bikin Sabuwar Shekara ta 2025, zamu sake zage dantse da ta hanyar ninka ayyukan da mukayi a baya. Muna da sabbin manufofi na kara kyautata wa nagartattun alummar mazabar Fufore da song a wannan shekarar ta 2025; kuma zamu jajirce wajen aiwatar da su domin amfanin al'ummar mu na Fufore/Song.

Shekarar da ta gabata ta gabatar ta kasance cuke da ƙalubale, amma duk da haka, mun cimma manyan nasarori tare da goyon bayanku da addu'o'in ku, waɗanda sune suka zama tushen nasarar mu.  


Shekarar taxo da jarabawa iri-iri wanda ta shafi daidaikun mutane da al’ummomi, mun fuskanci kowane irin kalubale, amma kuma mun samu damammaki iri-iri na kyautatawa al’ummarmu daga kangin talauci da rashin aikin yi.

Duk da matsananciyar matsalar kudi da ake ciki, mun tsaya tsayin daka duk bayan wata uku muna bada tallafi ga jama'ar mu, haka kuma duk mako muna bada tallafi daidai gwargwado. Kuma muna duk mai yiwuwa domin tabbatar da wanzar da hadin kan al’ummarmu da tabbatar da an yi shi cikin aminci da ci gaba. 
A wannan shekara ta 2025, mu kara hada kanmu, mu kara inganta alakar mu domin samun zaman lafiya, kamar yadda muka sani babu wani ci gaba dake samuwa ba tare zaman lafiya ba. Amincewar ku da mu shine yake bamu tabbacin cewa hakika muna kan hanya madaidaiciya.

Har yanzu muna gode wa Allah Madaukakin Sarki akan komai na shekarar ta 2024. Ina taya mu murna da kasancewar mu cikin wadanda ke raye don shaida wannan rana.

Ina addu'ar 2025 ya kara kawo maba ci gaba Mai dorewa da kuma samar da ayyukan yi ga kowa a mazabar Fufore/Song Abar kaunar mu, da jihar Adamawa, da kuma kasar mu ta gado Najeriya.

Saboda haka, ina yi mana fatan sabuwar shekara ta 2025 ya zame mana abun farin ciki da wadata!

Na gode, Allah ya saka da alheri.
Na kasance Dan ku Abokin ku Yayan ku kuma wakilin ku,
Hon. (Bar.) Aliyu Wakili Boya.
Mamba mai wakiltar mazabar Fufore/Song, kuma shugaban kwamitin hukumar Yan sanda a majalisar dokokin tarayya ta kasa.

Abubakar Sali
#boyamovingtrain

Comments

Popular posts from this blog

ALH BAMANGA DAWARE DISTRIBUTED DRY SEASON FARMERS EMPOWERMENTS AND WOMEN EMPOWERMENTS TO HIS PEOPLE ON BEHALF OF BOYA TODAY

MILLIONS OF NAIRA SHARED FOR SALLAH PACKAGE 📦 TO SOCIAL MEDIA HANDLERS FOR HON BRR ALIYU WAKILI BOYA

WELCOME ADDRESS PRESENTED BY HONOURABLE (BARR.) ALIYU WAKILI BOYA, CHAIRMAN, HOUSE COMMITTEE ON POLICE INSTITUTIONS DURING THE FLAG-OFF OF REHABILITATION OF JABBI LAMBA, MALABU, SARAU, AND BELEL ROAD THAT LINKED TO THE REPUBLIC OF CAMEROON.